Matashi zai auri mata biyu rana guda bayan ya dirka musu ciki

June 2024 · 2 minute read

Ughelli, Delta - Wani mutumi dan jihar Delta, kudancin Najeriya na gab da angwancewa da dirka-dirkan mata biyu lokaci guda.

Mutumin mai suna John Erere Nana zai auri yan matan masu suna Patience Boyi da Elohor Dudu ne bayan sun dauki juna biyu daga garesa.

A hotunan da Instablog9ja ya daura kan Instagram, an shirya auren gargajiyan ne a makarantar Firamaren Ishere dake Oviri Agbarho, karamar hukumar Ughelli North, jihar Delta.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Jihar Kano ta bi dare ta sake rufe ofishin lauyan Shekarau

Dukkansu yan jihar Delta, sun sanya irin kaya guda a hoton dake jikin katin gayyatan.

Yan Najeriya sun tofa albarkatun bakinsu:

Comrade S.N yace:

Kai wannan ba karamin jarumi bane gaskiya ..Bana shi zamu bawa kyautar Gwarzon Shekara a bisa wanga kokari da yayi✌

Khalid Hassan Abubakar:

Wannan shege ne, Shegantaka se Anna

Muktar Mahmud Muktar:

Lalle yayi kokari sosai

Saifullahi Sa'idu Gangara

Da an Bari sun haihu a had'a da Suna kawai

Aleeyou Habeeb Abdoulkhareem:

gwaji yayi kuma yanzu ya tabbatar da cewa ba juyoyi ze auro

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGlkaYNygJNmpJqskai1qrqMs5iiZZGqv6p5zJqrmmWSnsa2edGapZqqXZzCpa2Mm5iymZ5isaq%2Byppkpq2jqnqktcqiZg%3D%3D