Tirashi: Matashi an Kano Da Ya Auri Baturiya Ya Shiga Aikin Soja a Amurka

July 2024 · 3 minute read

US - Suleiman Isah, haifaffen cikin garin Kano da ya auri baturiya Janine Reimann, ya wallafa wani hoto a kafar sadarwa da ke nuni da cewa ya shiga aikin soja a ƙasar Amurka.

Suleiman dai ya wallafa hoton ne ranar Juma'a 12 ga watan Mayun 2023, a shafinsa na Facebook kamar yadda ya saba ɗora hotunansa a baya, gami da nuna godiya ga Ubangiji.

Kara karanta wannan

Abubuwa 20 da za a Rika Tuna Buhari da su Shekaru Bayan Barin Aso Rock - Hadiminsa

Ana cikin shekara ta 3 kenan da yin auren

A ranar 13 ga watan Disamban shekarar 2020, aka ɗaura auren Suleiman Isah wanda a lokacin ya ke da shekaru 23, tare da matar tasa Janine Reimann, baturiyar Amurka mai shekaru 46.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daily Nigerian ta wallafa cewa masoyan sun haɗu ne a kafar sadarwa ta Instagram watanni takwas baya kafin lokacin auren nasu.

Janine wacce ta kasance mai sana'ar abinci ce, wacce ke zaune a Lindon, da ke California ƙasar Amurka, a lokacin ta taso zuwa birnin Kano da ke arewacin Najeriya don shaida wannan ɗaurin aure.

Sanata Shehu Sani ne ya tsaya masa

Mutane da dama sun halarci ɗaurin auren wanda aka gudanar a masallacin barikin sojoji da ke Panshekara Kano. Daga cikin waɗanda suka halarta akwai tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani, wanda shine ya tsayawa angon a lokacin ɗaurin auren.

Kara karanta wannan

Ekweremadu Da Sauran Jerin Manyan 'Yan Siyasar Da Aka Taba Kullewa a Kasar Waje

Bayan ɗora hoton sanye da kakin sojan Amurka da Suleiman ya yi, mutane da dama sun yi tururuwa zuwa akwatinsa na ajiye sharhi don yi masa murna bisa wannan ci gaba da ya samu.

Kwamared Shehu Sani ma dai ya tofa albarkacin bakinsa, in da ya nuna godiya bisa ci gaban da Suleiman ya samu, saboda a can baya wasu sun yi masa shaguben cewa ya haɗa shi da baturiya amma kuma yanzu ga yadda ta kaya.

Kyakkyawar baturiya ta kai saurayinta su gana da surukansa

A wani labarin mai kama da wannan da muka wallafa a watan Maris, kun ji wata kyakkyawar baturiya da ta kai saurayinta ɗan Najeriya wajen iyayenta domin su gana.

Budurwar ta ce ta yi hakan ne saboda tunanin da ta ke na cewa ba dole iyayenta su amince da zaɓin saurayin da ta yi ba.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllaIF0gJZmq6Kqkai1qnnMmquaq5ieeqytzahknZldrq5urdSroGaakanCs7XYmmSymV2otaqzwGaYoqOZo3q0u8maZJplkaLCs7fAaA%3D%3D