- Akwai wani batu da ke yawo wanda ke cewa shugaban mulkin sojin ƙasar Mali ya yi barazanar farmakar birnin tarayya Abuja
- A cikin batun an bayyana cewa Kanal Goita ya yi barazanar farmakar birnin Abuja ne idan har ECOWAS ta aike da dakarunta zuwa Nijar
- Sai dai, binciken bin diddigi da a ka gudanar ya nuna cewa babu ƙamshin gaskiya a wannan batun da a ke yaɗa wa
Wani shafi a Facebook wanda aka sani da sunan Labour Party Plateau State Chapter, a nan ne aka yaɗa wani batu mai cewa ƙasar Mali ta bayyana cewa tana sane da ainihin wanda ya lashe zaben shugaban ƙasa na 2023, sannan ta yi barazanar ɗora wanda ya lashe zaɓen kan kujerarsa.
Wani ɓangare na rubutun na cewa
"Idan ECOWAS ta kuskura ta farmaki birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, ba wai za mu kawo ɗauki ba ne, amma za mu farmaki Abuja, babban birnin Najeriya, domin ɗora ainihin wanda ya lashe zaben shugaban ƙasa na 2023.""Yadda Na Yi Kwamishina, Minista Ba Tare Da NYSC Satifiket Ba": Na Hannun Daman Buhari Ya Fasa Kwai
A lokacin rubuta wannan rahoton, mutum 52 ne suka sake yaɗa wannan batun a Facebook.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abin da shugaban sojin Mali ya ce wajen yin haɗaka da Nijar
A binciken bayanin da Kanal Goita ya yi, gidajen watsa labarai da dama sun wallafa labarin, ciki har da tashar Cable News Network (CNN) ta ƙasar Amurka, Nigerian Tribune, da Voice of Nigeria (VON).
A cewar rahoton, Kanal Goita ya tabbatar da cewa ya yi waya da shugaban Rasha, Vladimir Putin, inda ya yi kiran a warware rikicin na Nijar cikin ruwan sanyi.
An kuma gano cewa ƙasashen Mali da Burkina Faso sun yi haɗaka da Jamhuriyar Nijar, kuma haɗakar ta su ta ƙunshi cewa dakarun sojojin ƙasashen za su iya kawo ɗauki idan aka farmaki ɗaya daga cikinsu.
Shugaba Tinubu Ya Tsige Babban Hadimi Daga Muƙaminsa, Ya Umarci Ya Dawo Gida Najeriya
Kanal Goita na Mali bai taɓa barazanar farmakar Abuja ba
An yi bincike a sauran kafafen watsa domin ganin ko akwai inda aka rahoto cewa Kanal Goita ya yi barazanar farmakar Abuja idan aka farmaki Jamhuriyar Nijar.
Sai dai, babu ɗaya daga cikin rahotannin wanda ya nuna cewa Goita ya yi barazanar cewa zai farmaki Abuja, tare da ɗora wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023 kan kujerar shugaban ƙasa.
Saboda haka, babu wani sahihin rahoto kan haɗakar wanda ya nuna Kanal Goita ya yi barazanar, sannan ƙasar Mali ministan harkokin ƙasashen wajenta ne ya wakilceta a Nijar wajen yin haɗakar.
An Bude Iyakokin Gabon
A wani labarin kuma, sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo na ƙasar Gabon, sun bayar da umarnin bude iyakokin ƙasar.
Sojojin sun sanar da cewa sun buɗe iyakokin ƙasar na ƙasa, sama, ruwa da isƙa domin cigaba da hada-hada kamar yadda aka saba.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllan9yg5BmmaKmk564pnnYmmSnrZ6Weqit0qSgspldoK6vecGaq66mXai1trPAm5inZZ2quay1zWaqqKKZo3qurcuiZLKZXa62bq7Aq5izmZ6Wv263wLCmZqCRp7ZurYyama6ikWQ%3D